Hukumar KAROTA ta tura jami’ai 1,000 domin daƙile cunkoso yayin bukukuwan Babbar Sallah a Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano, Kano Road Traffic Agency (KAROTA), ta sanar da tura jami’anta 1,000 zuwa wurare daban-daban a faɗin jihar domin tabbatar da daidaitacciyar zirga-zirga yayin bukukuwan Babbar Sallah.

Manajan Daraktan hukumar, Faisal Mahmud-Kabir, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Ibrahim-Sharada, ya sanyawa hannu ranar Litinin a Kano.

Sanarwar ta ce an tura jami’an ne zuwa manyan hanyoyi, filayen Idi, wuraren shakatawa da sauran wuraren taruwar jama’a domin rage cunkoso da tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan.

Hukumar ta bayyana cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen da ta ɗauka domin sauƙaƙa zirga-zirga da kare lafiyar masu amfani da hanyoyi a lokacin Babbar Sallah.

KAROTA ta kuma yi kira ga direbobi da sauran masu amfani da hanya da su ba jami’an zirga-zirga haɗin kai tare da bin dokokin hanya domin tabbatar da gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da tsaro.

Faisal Mahmud-Kabir ya yi fatan al’ummar jihar Kano za su gudanar da bukukuwan Babbar Sallah cikin lumana da aminci.

Comments (0)
Add Comment