Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bukaci gwamnatocin jihohin Najeriya su kara kudin da suke sanya wa a bangaren rigakafi domin karfafa samun allurar rigakafi a tsakanin al’umma, musamman bayan koma baya da aka samu sakamakon annobar COVID-19.
Daraktan WHO na rikon kwarya a Afrika, Dr Chikwe Ihekweazu, ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da makon rigakafi a Afrika da aka gudanar a jihar Ribas, yana mai jaddada cewa rigakafi hakki ne kuma jari ne ga lafiyar al’umma.
Ya bayyana cewa sama da yara miliyan shida a nahiyar Afrika ba su samu kowanne irin rigakafi ba a shekarar 2023, lamarin da ke barazana ga lafiyar al’umma tare da bazuwar cututtuka kamar sankarau da polio.
WHO ta bukaci a kara himma wajen cimma manufofin Shirin Rigakafi na 2030, tare da bukatar hadin kai daga gwamnati, da al’umma da kungiyoyin kasa da kasa don tabbatar da rigakafi ga kowa.