Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya haura naira biliyan 2.6 a Jihar Jigawa.
Shugaban hukumar a jihar, Musa Maina, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi da kayayyakin da aka kama a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jiha.
Maina ya bayyana cewa an gano kwayoyin ne a yankin Gumel, bayan wani samame na kwanaki uku a jihohin Jigawa da Kano.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin da suke ƙoƙarin rarraba kwayoyin zuwa Jihohin Jigawa, Yobe, Bauchi da kuma Jamhuriyar Nijar.
Kwayoyin da aka kama sun haɗa da tan 118.6 na ƙwayar Tramadol da kilo 195.3 na ƙwayar Pregabalin, tare da wasu ƙwayoyi daban-daban.
Maina ya bayyana wannan aikin a matsayin babbar nasara da aka cimma ta hanyar amfani da bayanan sirri, yana mai cewa hakan shi ne babban ci gaba da hukumar ta samu wajen yaƙi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.