Hukumar NiMET Tayi Hasashen Yanayin Da Zai Kasance Daga Ranar Talata Zuwa Alhamis

Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen cewa daga ranar Talata zuwa Alhamis za a samu gaurayen rana da gajimare a sassan ƙasar.

A cewar hasashen da aka fitar a Abuja, yankin Arewa zai fuskanci yanayi mai cike da rana a ranar Talata, yayin da yankin Tsakiya zai samu ɗan gajimare, kuma ana iya samun guguwar iska da ruwan sama a wasu sassan kudancin Jihar Kwara.

Yankin Kudu kuma ana sa ran zai samu rana da ɗan gajimare, tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama kaɗan a jihohi da dama ciki har da Legas, Oyo, Ogun, Osun, Edo, Ekiti, Ondo, Imo, Delta, Bayelsa, Akwa Ibom, Cross River da Rivers da yammacin rana.

A ranar Laraba, rahotanni sun ce yankin Arewa zai ci gaba da samun rana, yayin da yankin Tsakiya zai samu ɗan gajimare, tare da yiwuwar tsawa da ruwan sama kaɗan a kudancin Kogi, Benue da Kwara, yayin da yankin Kuduancin ƙasar zai fuskanci irin wannan yanayi na tsawa da ruwan sama a wasu jihohi.

Hasashen ranar Alhamis ya nuna cewa yankin Arewa zai samu rana da ɗan gajimare, tare da ƙaramar yiwuwar tsawa a wasu sassan Kwara da safe, yayin da yankin Kudun ƙasar zai samu tsawa da ruwan sama kaɗan a Bayelsa da Cross River.

NiMet ta shawarci jama’a da su ɗauki matakan kariya saboda ƙura a sararin samaniya, musamman masu cututtukan numfashi, tare da jan hankali ga direbobi da su yi taka-tsantsan a lokacin ruwan sama, kuma kamfanonin jiragen sama su riƙa neman rahotannin yanayi na filayen jirgi domin gudanar da ingantaccen shiri.

Comments (0)
Add Comment