Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Kano ta aurar da wasu mata da suka musulunta inda ta dauki nauyin aurensu

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta aurar da wasu mata da suka musulunta, inda ta dauki nauyin aurensu; da saya musu gadajensu da sauran kayan daki da kayan kicin.

Daraktan gudanarwa na hukumar, Auwal Lamido, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa yau a Kano cewa hukumar ta kuma warware wasu kararraki bakwai da suka shafi rikicin shugabanci a masallatai da makarantun Islamiyya cikin watanni biyu.

A cewar daraktan, an warware matsalolin a watan Maris da Afrilu na wannan shekara.

Auwal Lamido ya bukaci jama’a da su tabbatar suna yin dabi’u masu kyau da tsoron Allah SWT a cikin mu’amalarsu.

An kafa hukumar ne a shekara ta 2001 a matsayin ofishin kula da harkokin zamantakewa na musulunci, amma an daga darajarta zuwa Hukumar Shari’a a ranar 7 ga Nuwamban 2003.

Aikinta shi ne dabbakawa, tursasawa da kuma inganta dabi’un addinin musulunci da na al’adu a jihar.

Comments (0)
Add Comment