Hukumomi a Saudiyya sun ce ba a ga watan Shawwal ba a yau Asabar za a yi Azumin Ramadana guda talatin cif-cif

Masana ilimin taurari sun yi hasashen cewa ba za a ga jaririn watan Shawwal ba a yau Asabar saboda wata zai riga rana faɗuwa kamar yadda suka tabbatar.


Saboda haka, hukumomi a Saudiyya sun ce ba a ga watan Shawwal ba a yau Asabar, abin da ke nufi za a yi Azumin Ramadana guda talatin cif-cif (30).

Comments (0)
Add Comment