Hukumomin Tsaron Ghana Sun Cafke Mutane 53 da Ake Zargi da Aikata Manyan Laifukan Intanet

Hukumomin tsaron Ghana sun cafke mutane 53 da ake zargi da aikata manyan laifukan intanet a wani gagarumin sumame da suka kai cibiyoyin aikata laifukan intanet a birnin Accra da wasu yankuna da ke kewaye da birnin.

A cewar rahotanni, daga cikin mutanen da aka kama, mutum 44 an bayyana cewa an yaudare su ne aka shigar da su ƙasar Ghana da sunan samun aiki, sai dai daga bisani aka tilasta musu shiga harkar aikata laifukan intanet. Hukumomin tsaro sun ce sun samu nasarar ceto waɗannan mutane daga hannun masu tilasta musu aikata laifukan.

Rahoton ya kuma nuna cewa dukkan mutanen 53 da aka kama ’yan asalin Najeriya ne. Hukumomin tsaron Ghana sun ce bincike na ci gaba domin gano waɗanda ke da hannu a shirya wannan harkar da kuma ɗaukar matakan doka da suka dace.

Comments (0)
Add Comment