Idan Amurka ta sake kai mana hari, za mu mayar da martani mafi muni – Iran
Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta gargaɗi Amurka cewa za ta fuskanci martani mai tsanani idan ta sake kai hare-hare, bayan abin da ta bayyana a matsayin harin da Amurka ta kai kan gaɓar tekunta.
A wata sanarwa da IRGC ta fitar, ta zargi Amurka da kai hare-haren sama kan wasu wurare a gaɓar tekun Iran, lamarin da ta ce ya biyo bayan farmakin da aka kai kan wani jirgi a mashigar ruwan Hormuz, wanda Iran ke ganin ya bi hanyar da ba ta halatta ba.
Iran ta ce wannan mataki na Amurka ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma alƙawuran da ta ɗauka, tana mai jaddada cewa hakan ya sa ta ɗauki mataki na mayar da martani.
Sai dai IRGC ba ta bayyana cikakken bayani kan wuraren da aka kai hare-haren ko irin ɓarnar da aka samu ba, amma ta ce kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz na karkashin alhakinta ne bisa wasu yarjejeniyoyi.
A ƙarshe, Iran ta sake jaddada cewa idan aka sake yin irin waɗannan hare-hare, martanin da za ta mayar zai fi tsauri, abin da ke nuna ƙarin tsanantar rikici a yankin.