Idan Na Ci Zaɓe Zan Sasanta da ’Yan Bindigar da Suka Shirya Ajiye Makamai — Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi a 2027, gwamnatinsa za ta sasanta da ’yan bindiga da sauran masu tayar da ƙayar baya da suka ajiye makamai suka rungumi zaman lafiya.

Sai dai Obi ya nanata cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin soja kan waɗanda suka ci gaba da rusa tsarin zaman lafiya da aminci a ƙasar.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da ɗan jaridar nan Rufai Oseni a ranar Talata.

Tsohon gwamnan Jihar Anambra ya ce ɗorewar zaman lafiya na buƙatar buɗe ƙofar tattaunawa ga duk wani mutum ko ƙungiya da ke da niyyar komawa kan hanya madaidaiciya da bayar da gudummawa wajen gina ƙasa.

A cewarsa, “duk wanda yake son zaman lafiya zan tattauna da shi, zan sasanta da shi. Amma wanda yake son tashin hankali, za mu yi yaƙi da shi.”

Ya kuma ce haɗin kan Najeriya ba zai samu ba sai an tabbatar da adalci da ba wa kowa damar sharɓar romon dimokuraɗiya ba tare da nuna bambanci ba.

Domin jaddada hujjarsa ta sansantawa da waɗanda suka rungumi zaman lafiya, Obi ya bayar da misali da wata ziyara da ya kai wata jami’a a ƙasar Amurka, inda ya ce wasu daga cikin shugabannin makarantar sun taɓa fuskantar zaman kurkuku kafin daga bisani su sake gina rayuwarsu da matsayinsu.

“Na taɓa zuwa wata jami’a a Amurka inda dukkanin shugabannin makarantar mutane. E da suka fito daga kurkuku.

“Daga shugaban makaranta har zuwa sakatare da malamai sun yi zaman shekaru a kurkuku saboda laifuka daban-daban.”

Ɗan takarar ya kuma danganta batun tsaro da haɗin kan ƙasa, yana mai jaddada cewa dole ne kowane yanki ya ji cewa yana da wakilci a gwamnati da ci gaban ƙasa.

Ya ce hangen nesan da yake yi wa Najeriya ya ta’allaƙa ne kan haɗa kan al’umma, adalci da daidaito wajen rabon damammaki, ta yadda babu wata ƙabila ko wani yanki da zai yi zargin an mayar da shi saniyar ware.

“Zan haɗa ƙasa in tabbatar cewa babu wanda aka bari a baya. Babu wata ƙabila da za a bari a baya; za a samu haɗin kai. Za mu nuna soyayya da kulawa ga kowa,” in ji Obi.

Wannan batu dai na ƙara haifar da muhawara kan wace hanya ce ta fi dacewa wajen magance matsalar tsaro da ke addabar Najeriya, tsakanin tattaunawa, amfani da ƙarfin soja ko haɗa hanyoyin biyu.

A gefe guda kuma, wasu masu sharhi na ganin tattaunawa na iya zama wani ɓangare na samar da zaman lafiya, yayin da wasu ke gargaɗin cewa yin sulhu da masu ɗauke da makamai na iya ƙara wa masu laifi ƙwarin gwiwa, sannan kuma ya daƙile ƙoƙarin da jami’an tsaro suke yi na dawo da doka da oda.

Comments (0)
Add Comment