Fitaccen mawakin Afrobeats ɗin nan na Najeriya, Davido, ya sake jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan wani bidiyo nasa ya karaɗe intanet inda yake bayyana yawan kuɗin da yake karɓa wajen gudanar da wasa.
A cikin bidiyon da ya bazu sosai, mawakin ya bayyana cewa yana karɓar dala $600,000, kwatankwacin sama da naira miliyan 825, a duk wani wasa da zai gudanar, gwargwadon canjin kuɗi.
Davido ya kuma ce yana yin aƙalla wasanni huɗu a kowane wata, lamarin da ya sake nuna irin girman kasuwancin waƙar Afrobeats da kuma yadda mawakan Najeriya ke samun karɓuwa a duniya.