India za ta hukunta masu hannu wajen kai hari a yankin Kashmir

Ministan harkokin wajen India ya ce za a hukunta waɗanda suke da hannu a shiryawa da kai mummunann harin da aka kai yankin Kashmir.

Sanarwar Subrahmanyam Jaishankar na zuwa ne, bayan tattaunawar da sukai da takwaransa na Amurka, Marco Rubio.

Mr Rubio ya kira India da Pakistan ta wayar tarho a jiya Laraba, domin ƙoƙarin kwantar da tashin-tashina da zaman ɗarɗar da ake yi tsakanin ƙasashen biyu.

India dai ta zargi Pakistan da goyon bayan maharan, zargin da ta musanta inda wani ministan gwamnatin ya ce ba za su naɗe hannu su zuba ido ba.

Ya ce ya kamata ƙasashen waje su kalli abin da ke faruwa su san haƙƙin abin da zai biyo baya ya rataya ga India, wadda ke son tashin hankali da rura wutar rikicin.

Comments (0)
Add Comment