INEC ta ƙara wa’adin rajistar masu zaɓe da sati biyu
Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta sanar da ƙara wa’adin ci gaba da rajistar masu zaɓe na tsawon makonni biyu, domin bai wa ‘yan Najeriya da suka cancanta ƙarin damar yin rajista.
A wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu, INEC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan nazarin yadda aikin rajistar ke gudana da kuma la’akari da ra’ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar ta bayyana cewa aikin rajistar wanda ya fara a ranar 18 ga Agustan 2025, kuma aka shirya kammala shi a ranar 10 ga Yulin 2026, yanzu zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi 26 ga Yulin 2026.
INEC ta kuma sanar da ƙaddamar da tsarin rajistar kai tsaye ta intanet ga masu yin rajista karo na farko.
Hukumar ta ce daga ranar 8 ga Yulin 2026, masu son yin rajista za su iya amfani da shafinta na intanet domin kammala rajistar.