INEC ZA TA TURA ’YAN NYSC MILIYAN 1.4 A ZAƁEN 2027

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta bayyana cewa za ta tura sama da matasan NYSC miliyan 1.4 domin taimakawa wajen gudanar da babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Joash Amupitan, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa babban daraktan NYSC, Olakunle Nafiu, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Ya ce shirin wani bangare ne na shirye-shiryen da INEC ke yi tun da wuri domin tabbatar da sahihin zaɓe cikin tsari da inganci.

INEC dai na amfani da mambobin NYSC a matsayin ma’aikatan wucin gadi a lokutan zaɓe, musamman wajen rajistar masu kaɗa ƙuri’a, tantance masu zaɓe da kula da rumfunan zaɓe a faɗin ƙasa.

Comments (0)
Add Comment