IOM Ta ƙaddamar da shirin farfaɗo da al’umma a Katsina da Zamfara domin magance rikice-rikice

A wani cigaban kuma, Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, IOM, ta ce fiye da mutane miliyan 1.3 ne rikice-rikicen tsaro suka raba da muhallansu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya zuwa watan Fabrairu na bana.

A yayin kaddamar da wani sabon shiri da Tarayyar Turai ta tallafa a Katsina, shugabar hukumar a Najeriya, Dimanche Sharon, ta ce shirin zai magance tushen rikici ta hanyar inganta zaman lafiya a tsakanin al’umma, zamantar da aikin gona domin kare muhalli, da kuma shirye-shiryen sulhu da al’umma.

Ta ce wannan zai baiwa jama’a damar farfado da hanyoyin samun abinci da aikin yi tare da ƙara amincewa da shugabancin ƙananan hukumomi, musamman a Katsina da Zamfara inda aka kauracewa gonaki da kauyuka da dama.

Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Gautier Migno, ya tabbatar da ci gaba da tallafi tare da hadin gwiwa da IOM da kungiyoyin cikin gida, yayin da gwamnan Katsina Dikko Radda ya bayyana shirin a matsayin alamar haɗin kai da jajircewar dawo da martaba da zaman lafiya a yankin da ke fama da rikici.

Comments (0)
Add Comment