Isra’ila Ta Ce Mutum 6,000 Ne Suka Jikkata Sakamakon Hare-Haren Iran

Ma’aikatar Lafiyar Isra’ila ta ce kawo yanzu aalla mutum 6,000 ne aka kwantar da su a a asbiti sakamakon hare-haren Iran.

Ma’aikatar ta ce har kawo yanzu akwai mutum 121 da ake kula da su a asibitoci, inda mutum aya yake cikin mummunan hali sannan 16 ke yanayin mutu kwakwai rai kwakwai.

Ma’aikatar ta lafiya ta kuma ara da cewa an kai wasu ƙarin mutum 232 da suka jikkata zuwa asibitoci cikin dare.

Comments (0)
Add Comment