Isra’ila Ta Ce Za Ta Ruguje Wasu Kauyuka A Lebanon

Ministan tsaron Isra’ila ya ce sojojin Isra’ila za su ruguza dukkanin gidaje a kauyukan Lebanon da ke kusa da kan iyakar Isra’ila.

Isreal Katz ya ce sojojin za su ci gaba da iko da wani yanki mai fadi, har zuwa kogin Litani, ko da an kawo karshen rikicin da suke yi da Hizbullah.

Ministan ya ce za a hana sama da mazauna Lebanon dubu dari shida da suka rasa matsugunansu komawa gida har sai an tabbatar da tsaron mazauna arewacin Isra’ila.

Fira Ministan Canada Mark Carney ya bayyana matakin a matsayin keta haddin iyakokin ƙasar Lebanon.

Comments (0)
Add Comment