Ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) ta naɗa Abu Khalifa a matsayin sabon kwamandanta a yankin da ake kira Timbuktu Triangle.
Wannan naɗin ya biyo bayan kashe tsohon kwamandan ISWAP, Julaibib, da sojojin Najeriya na Operation HADIN KAI suka yi a Kimba, ƙaramar hukumar Damboa a Jihar Borno.
Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana a cikin wani rahoto da ya fitar ranar Litinin cewa an yi wannan naɗi ne bayan tattaunawar cikin gida a tsakanin shugabannin ISWAP.
A cewarsa, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an kawar da Julaibib ne a wani sumamen soji da aka kai a yankin Kimba na Damboa LGA, lamarin da ya tilasta wa ƙungiyar sake tsara shugabancinta cikin gaggawa.
“Bayanan sirri sun nuna cewa an naɗa Abu Khalifa a matsayin sabon kwamandan ISWAP a Timbuktu Triangle domin maye gurbin Julaibib,” in ji majiyar.
An kuma gano cewa har yanzu ba a naɗa mataimakin kwamanda (2IC) a hukumance ba.
Sai dai majiyar ta ƙara da cewa wani mutum mai suna Tuja na samun karɓuwa a tsakanin mayakan ƙungiyar a matsayin wanda aka fi kallon zai zama mataimakin kwamanda.
Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Operation Hadin Kai ke ci gaba da kai hare-hare masu ɗorewa kan sansanonin ISWAP da Boko Haram a sassan kudancin Jihar Borno.