Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga Biyu, Sun Kuma Dakile Harin da Aka Yi da Rana Tsaka A Kano

Wani hari da ‘yan bindiga masu hawa babura ɗari-ɗari suka kai da rana tsaka a wani garin iyaka a Kano ya gamu da cikas, bayan da haɗin gwiwar jami’an tsaron Najeriya tare da Kano Civilian Joint Task Force suka dakile harin, suka kuma ceto sama da shanu 500 da aka sace tare da kashe aƙalla mutum biyu daga cikin maharan.

Da yake bayyana lamarin ta wayar tarho, shugaban Kwamitin Tsaron Al’ummar Faruruwa, Alhaji Yahya Bagobiri, ya yaba da saurin martanin jami’an tsaro, musamman ‘yan sanda, inda ya ce ya tattauna da Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori.

Ya ce: “’Yan bindigar da suka kai kusan babura 150 sun kai hari garin Tsauri da ke ƙaramar hukumar Shanono a jihar, inda suka nufi wani Bafulatani mai shanu sama da 2,000, suka sace kusan dukkansu amma ba su samu shi ba.

“Da muka samu labarin abin da ke faruwa, nan da nan muka sanar da jami’an tsaro, sannan muka faɗakar da garuruwan da ke kusa kamar Goron Dutse, Shanono, Tsanyawa da sauransu, yayin da ni kuma na kira Kwamishinan ‘Yan Sanda wanda ya bayar da umarnin daukar matakin gaggawa.”

Bagobiri ya ƙara da cewa haɗin gwiwar jami’an tsaro sun yi saurin isa wurin, inda suka tare ‘yan bindigar yayin da suke ƙoƙarin tserewa da shanun da suka sace, wasu na kokarin shiga Katsina wasu kuma suna cikin Kano. Jami’an tsaron sun bi su, suka kashe kimanin biyu daga cikin maharan, tare da kwato shanu 500.

Comments (0)
Add Comment