Jami’ar Abuja Ta Kori Ɗalibai 28 Kan Laifukan Ƙungiyoyin Asiri, Maguɗin Jarabawa, Ƙwayoyi da Barazanar Kisa

Majalisar Dattawan jami’ar Abuja ta amince da korar ɗalibai 28 daga jami’ar bisa laifuffukan da suka haɗa da ƙungiyoyin asiri, satar ansa a jarabawa, mallaka da amfani da miyagun ƙwayoyi, da kuma barazanar kisa.

An yanke hukuncin ne a taron Majalisar na 191 na yau da kullum, bayan nazarin rahoton Kwamitin Ladabtar da Ɗalibai.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Dakta Habib Yakoob, ya fitar a ranar Lahadi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Sanarwar ta ce an same su da aikata manyan laifuffuka da haɗa baki wajen aikata laifi, fasa ɗaki da sata, ƙirƙirar takardun sakamakon jarabawar ‘O’ Level na bogi da aka ɗora a manhajar jami’ar domin neman gurbin karatu, da kuma mallaka da amfani da miyagun ƙwayoyi.

Majalisar ta kuma amince da soke takardun shaidar kammala karatu da aka bai wa tsofaffin ɗalibai 15, bayan sun ƙi amsa gayyatar kwamitin ladabtarwa sau da dama.

Sai dai an wanke ɗalibai tara bayan bincike, yayin da aka yiwa  wasu 33 gargaɗi kan laifuffuka irin su damfarar ɗalibai ɗakunan kwana, da faɗa.

Da yake jawabi kan matakin, Mataimakin Shugaban Jami’a kuma Shugaban Majalisar, Farfesa Hakeem Fawehinmi, ya ce jami’ar ba za ta sassauta kan ƙa’idojinta ba ko kuma ta lamunci duk wani abu da zai tauye mutuncin ilimi ba.

Ya ce, sun kuduri aniyar hukunta duk wanda ya karya dokoki yadda ya kamata.

“Burimmu ba wai ladabtarwa kaɗai ba ce, har ma da jagorantar ɗalibai zuwa zama nagartattun ’yan ƙasa da kuma cimma ƙwarewar ilimi.”

Ya ƙara da cewa jami’ar na ci gaba da ƙoƙarin samar da muhalli mai aminci da dacewa ga karatu wa ɗalibai da ma’aikata, tare da ƙarfafa shirye-shiryen wayar da kai, shawarwari da tarurruka domin hana aukuwar irin waɗannan laifuffuka a gaba.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar ƙungiyoyin asiri, satar ansa a lokutan jarabawa da sauran laifuka a manyan makarantu a faɗin ƙasar.

Comments (0)
Add Comment