Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, yana da cikakken ’yancin mara wa duk ɗan takarar da yakeso baya a kowace jam’iyya, bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Da yake magana a wata hira da tashar Channels Television a shirin Morning Brief, Sakataren Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce babu laifi a matakin da Wike ya ɗauka na goyon bayan ’yan takarar APC a zaɓen ƙananan hukumomin FCT da aka gudanar a ranar 21 ga Fabrairu.
Maganar na zuwa ne bayan cece-kuce kan rawar da ministan ya taka a zaɓen, inda aka ce wasu ’yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyu Julius Adamu na Bwari da Zadna Dantani na Abuja Municipal Area Council sun janye takararsu tare da bayyana goyon baya ga abokan hamayyarsu na APC, bayan wata tattaunawa da aka ce Wike ya shiga ciki.
Kwamitin gudanarwar PDP ta ƙasa ta soki matakin, tana mai bayyana shi a matsayin abin kunya da kuma saɓawa dimokuraɗiyya, tare da zargin cewa an tilasta janyewar ba tare da amincewar jam’iyya ba.
Goyon bayan da Wike ya nuna wa ’yan takarar APC ya tayar da muhawara kan batun biyayya ga jam’iyya, sauya sheƙa da kuma iyakokin alaka a tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya.
A gefe guda kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da rawar da Wike ya taka a nasarar da APC ta samu a zaɓen FCT da kuma wasu zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a Jihar Rivers.