Jam’iyyar APC Ta Tabbatar Da Umar Namadi Ɗanmoɗi A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Jigawa Ba Tare Da Hamayya Ba

Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ta tabbatar da Gwamna Malam Umar Namadi Ɗanmoɗi, FCA a matsayin ɗan takarar gwamna babu hamayya domin tunkarar zaɓen 2027.

Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Isa Sadiq Achida ne ya bayyana hakan yayin wani gangami da aka gudanar a birnin Dutse ranar Alhamis.

Achida ya ce Malam Umar Namadi ya zama ɗan takarar jam’iyyar kai tsaye bayan babu wani mutum da ya tsaya takarar kujerar gwamna a ƙarƙashin APC a jihar.

Malam Umar Namadi Ɗanmoɗi ya karɓi mulki daga tsohon gwamna Alhaji Muhammadu Badaru Talamiz a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma yanzu yana neman wa’adi na biyu domin ci gaba da jagorantar jihar.

Comments (0)
Add Comment