JAM’IYYAR APC ZA TA TALLAFAWA WADANDA SUKA BA WA JAM’IYYA GUDUNMAWA BA TARE DA SUN AMFANA DA KOMAI BA A JIHAR JIGAWA

Shugaban Kwamitin Tuntuba da Karfafa Dangantaka tsakanin shugabannin kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki na APC a Jigawa, Alhaji Mohammed Saminu Yahaya, ya bukaci shugabannin kananan hukumomi da jiga-jigan jam’iyya su rika gano tare da karfafa mutanen da ke yi wa jam’iyya hidima ba tare da sun sami wani anfani ba kai tsaye ba.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai kananan hukumomin Dutse, Ringim da Jahun, inda ya ce Gwamna Malam Umar Namadi ya umurci kwamitin da ya hada kan shugabanni da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar APC a zaben 2027.

Alhaji Mohammed Saminu Yahaya ya ce manufar ziyarar ita ce karfafa hadin kai da fahimtar juna tsakanin shugabannin kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki, ba wai neman laifin kowa ba.

Comments (0)
Add Comment