JICORAS Babura ta gudanar da taron tantance ‘yan kwangilar da za su gina dakunan horaswa guda biyar a makarantar

Kwalejin Kimiyya da share fagen shiga Manyan Makarantu ta Jihar Jigawa da ke Babura, wato Jigawa State College of Remedial and Advanced Studies, ta gudanar da budaddiyar tantancewar bayar da kwangilar gina dakunan horaswa guda biyar a harabar makarantar.

A yayin gudanar da tantancewar, kamfanoni guda hudu ne suka shiga tsarin neman kwangilar domin gudanar da aikin gina dakunan horaswar.

Daraktan Ayyuka da harkokin gudanarwa na makarantar, Injiniya Madaki Gadama, ne ya tabbatar wa mahalarta taron cewa an bi dukkan ka’idoji da dokokin Hukumar Saye da Bayar da Kwangiloli ta gwamnati wajen zakulo kamfanin da ya cancanci samun kwangilar.

Ya ce an gudanar da tsarin cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da an bai wa wanda ya dace aikin.

A nasa jawabin, shugaban kwalejin, Dakta Ma’aji Abubakar, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin tarihi ga makarantar, yana mai cewa wannan ce kwangila mafi girma da aka taba bayar da shawarar amincewa da ita a tarihin kwalejin.

Dakta Ma’aji Abubakar ya shawarci kamfanonin da suka samu nasarar kwangilar da su tabbatar sun bi ka’idojin aikin tare da samar da ingantaccen aiki mahadi ka ture.

Sauran ayyukan da aka bayar da shawarar amincewa da su sun hada da aikin bayar da shawarwari kan gina dakunan horaswar, da kuma gyaran cibiyar fasahar sadarwa ta al’umma ta Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Kasa, wato National Information Technology Development Agency (NITDA).

Comments (0)
Add Comment