Hukumar UNICEF ta bayyana cewa jihohin Jigawa, Kano da Katsina ne ke da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makarantar boko a Arewacin Najeriya.
A cewar hukumar, jihohin uku na bayar da kusan kashi 30 cikin 100 na yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya, wadda ke kan gaba a duniya wajen yawan yaran da ba sa karatu.
Masaniyar ilimi ta UNICEF, Aisha Abdullahi, ta danganta matsalar da talauci, rashin tsaro da kuma wasu al’adu, tare da jaddada muhimmancin ilimin yara tun daga matakin farko.
Hukumar ta kuma yi kira ga iyaye da gwamnatoci da su kara himma wajen tallafa wa harkar ilimi domin rage yawan yaran da ke gararamba a tituna da kuma barin makaranta.