Jihar Bauchi ta kai ziyara Jigawa domin koyon tsare-tsaren kiwon lafiya

Wata tawaga daga gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Sani Muhammad, ta kai ziyara jihar Jigawa domin nazarin wasu tsare-tsare da manufofin gwamnati a ɓangaren kiwon lafiya da inganta abinci mai gina jiki.

Rahotanni daga Gidan Rediyon Jihar Jigawa sun bayyana cewa tawagar ta kai ziyarar ne domin duba yadda gwamnatin Jigawa ke gudanar da shirye-shiryen kula da lafiya da kuma samar da ingantaccen tsarin abinci mai gina jiki, da nufin anfani da irin tsarin a jihar Bauchi.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Dr. Sani Muhammad ya ce gwamnatin Bauchi na da burin ƙarfafa harkokin lafiya a jihar, saboda haka ta ga dacewar koyon wasu dabaru da Jigawa ke amfani da su wajen bunƙasa lafiyar al’umma.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Bauchi a shirye take ta haɗa hannu da gwamnatin Jigawa domin musayar ilimi, ƙwarewa da tsare-tsaren da za su taimaka wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a jihohin biyu.

A nasa jawabin, Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana jin daɗinsa kan ziyarar tawagar ta Bauchi, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da marawa duk wata haɗin gwiwa baya domin bunƙasa harkokin lafiya.

Gwamnan ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin jihohi wajen tsara manufofi da musayar dabaru zai taimaka wajen samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya da walwalar al’umma.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Jigawa a shirye take ta yi aiki tare da Bauchi wajen aiwatar da manufofin da za su amfani jama’a musamman a ɓangaren lafiya da abinci mai gina jiki.

Comments (0)
Add Comment