Kafa ‘yan sandan jihohi zai bawa gwamnonin jihohi damar tunkarar kalubalen tsaro

Shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce kafa ‘yan sandan jihohi zai baiwa gwamnonin jihohi damar tunkarar kalubalen tsaro a yankinsu.

Ya ce yanayin tsarin jami’an tsaron a halin yanzu ya sa gwamnonin ke san wahala wajen yin amfani da karfinsu akan soji domin tsaron jihohinsu.

Sai dai Gwamna Inuwa Yahaya ya lura cewa al’amari ne da ya shafi tsarin mulki wanda dole ne a bi ta hanyoyin da doka ta tanada.

Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Tinubu bisa yadda ta kuma nuna goyon bayanta ga wannan manufa tare da bayyana kwarin gwiwar cewa majalisar dokokin kasar nan za ta gaggauta daukar mataki kan lamarin, domin a cewarsa gwamnonin jihohi a shirye suke su ba da cikakken goyon bayansu.

Comments (0)
Add Comment