Kamfanin CBEX da ake zargin ya gudu da kuɗaɗen jama’a ya dawo aiki

Kamfanin hada-hadar kuɗin Crypto a Najeriya da ake zargin ya gudu da kuɗaɗen jama’a ya dawo aiki.

Ana zargin kamfanin ya damfari mutane sama da dubu 600 yawan kuɗaɗen da ya kai triliyan 1 da biliyan 200.

Mamallaka kamfanin sun ce a shirye suke su biya mutanen da suka rasa kuɗaɗensu nan ba da jimawa ba, amma sai ya tara sabbin abokan hulɗa da zasu sake amince su zuba kuɗaɗensu.

Wannan matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar EFCC ta wallafa bayanan mamallaka kamfanin su shida, inda ta sanar da nemansu ruwa a jallo.

Babban abinda ke ɗaukar hankalin jama’ar ƙasar yanzu haka shine yadda kamfanin ya sami ƙwarin gwiwar ci gaba da aiki, bayan tafka wannan gagarumin laifi, da kuma yadda jami’an tsaro ke iƙirarin neman jami’an kamfanin.

Comments (0)
Add Comment