Kamfanin man fetur na kasa ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su firgita saboda karancin man fetur

Kamfanin man fetur na Kasa ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su firgita saboda karancin man fetur kasancewar akwai sama da lita miliyan dubu 1 da miliyan 700 na man fetur.

A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Garba Deen Muhammad, kamfanin man na kasa ya ce bai kamata a sanya fargabar karancin man fetur a duk lokacin bukukuwan karshen shekarar da kuma bayan haka ba.

Sanarwar ta kuma ce, kamfanin na NNPC bashi da wata masaniya kan wani shiri da gwamnati za ta yi na haifar da karin farashin man fetur.

Sanarwar ta kara da cewa, ana shawartar jama’a da kada su razana suke sayen man fetur domin adanawa.

Comments (0)
Add Comment