Kamfanin simitin BUA, daya daga cikin manyan kamfanonin siminti a Afirka ta Yamma, ya shirya assasa wani katafaren kamfanin simiti da kamfanin samar da wutar lantarki a kananan hukumomin Guyuk da Lamurde na jihar Adamawa.
- Buratai ya nuna goyon bayansa ga kin bari sojojin kasashen waje su kafa sansani a Najeriya
- Shugaba Tinubu ya umarci duka hukumomin gwamnati da su sayi motoci masu amfani da iskar gas
- Akalla mutane 24 ne suka mutu sanadiyyar wani gini da ya ruguje a ƙasar Afrika ta Kudu
- Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta kubutar da wasu fasinjoji 17 da aka sace a jihar Katsina
- EFCC ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da damfara ta intanet a jihar Ribas
An sanar da haka lokacin da shugaban kamfanin BUA, Abdul-Samad Rabi’u, ya jagoranci tawagar manajojin kamfanin zuwa wata ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a gidan gwamnati dake Yola Babban birnin jihar.
Abdul-Samad Rabi’u yace binciken farko ya nuna cewa kananan hukumomin biyu suna da arzikin limestone mai inganci, kuma kamfanin BUA a shirye yake ya zuba jari a jihar.