Karamar hukumar Guri ta amince da aikin girka famfunan ruwa guda 3 a yankunan karamar hukumar

Shugaban karamar hukumar, Hon Abubakar Umar Danbarde, ya bayyana cewa sun amince da aikin girka famfunan ruwa guda uku a asibitin PHC na Dagana, da Unguwar Abuja B da kuma Unguwar Sukuma a Arin.

A cewar Danbarde, aikin yana cikin tsare-tsaren wannan watan da suka amince da su domin samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar karkara da birane.

Ya bayyana cewa ana sayen kayan gyaran famfo kullum domin gyara da wanda aka riga aka kafa a yankunan daban-daban.

Ya jinjinawa goyon bayan da suke samu daga gwamnan jihar, yana mai cewa hakan ne ke basu damar aiwatar da ayyuka da suka shafi rayuwar jama’a.

Comments (0)
Add Comment