Karamin ministan gidaje ya bayyana sharadin da zai sanya su karbi Rabiu Musu Kwankwaso a jam’iyyar APC

Wasu shugabannin APC a jihar Kano, ciki har da ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Ata, sun yi magana kan yiwuwar komawar Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar. Jiga-jigan na APC sun nuna rashin amincewa da shirin sauya sheƙa da tsohon gwamnan na jihar Kano, ke yi daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ba su maraba da Rabiu Musa Kwankwaso a APC, Kwankwaso bai da wani tasiri shiyasa yake so ya samu mafaka a jam’iyyar APC mai mulkin kasa ya nuna cewa jar hula ta Kwankwaso ta zama tarihi a Kano, domin a yanzu maganar APC kawai ake yi.

Yusuf Ata ya yi magana da manema labarai ne bayan wani taro da suka yi da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Comments (0)
Add Comment