Kasar Faransa ta kwace kusan Euro miliyan 850 na kadarorin kasar Rasha a cikin kasarta

Kasar Faransa ta kwace kusan Euro miliyan 850 na kadarorin kasar Rasha a cikin kasarta, a cewar ministan kudin Faransa.

Hakan na nufin masu kamfanin oligarch ba za su iya, sayar wa ko morar dukiyarsu ba.

Tun bayan da Rasha ta fara yakinta a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu kasashen yammacin duniya suka mayar da martani ga kasar cikin tsattsauran takunkumai tattalin arziki.

A ranar Juma’a, babban bankin kasar Rasha ya ce girman takunkumin zai sanya kasar cikin tattalin arziki mai matukar wahala.

Kwanaki 4 bayan da aka fara mamayar gwamnatin Rasha ta kara kudin ruwanta daga kashi 9.5 zuwa kashi 20 cikin 100 awani yunkuri na samarwa kanta mafita saboda mamayar.

Comments (0)
Add Comment