Kimanin mutum 500,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a yankuna 6 na Kasar Sudan ta Kudu

Kimanin Mutane dubu 500,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a yankuna 6 na Kasar Sudan ta Kudu a Cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Daga cikin wuraren 6 da ambaliyar ta shafa sun hada da Western Equatoria, Warrap, Northern Bahr El- Ghazal kuma yankuna biyu masu arzikin man fetur.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu 426 ne ambaliyar ta shafa a kudan cin Sudan tun cikin watan Mayu na wannan shekara.

Majalisar ta ce ambaliyar ta daidaita garuruwa da dama, wanda hakan ne ya tirsasawa mutanen samun mafaka a Chochi da kuma Makarantu.

Majalisar tace mutanen suna bukatar kanyan jinkai da kuma abinci.

Comments (0)
Add Comment