KISAN GILLA: ‘YAN SANDA SUN KAMA SABUWAR AMARYA KAN ZARGIN ZUBAWA MIJINTA GUBA A CIKIN ABINCI WANDA TAKAI DA YA RASA RANSA

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta tabbatar da kama wata sabuwar amarya bisa zargin zubawa mijinta guba a cikin abincin rana, lamarin da ya yi sanadin rasuwar mijin nata.

A cewar bayanin rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Janairu, 2026, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a ƙauyen Gauza, Karamar Hukumar Jahun, Jihar Jigawa.

Rahotannin binciken farko sun nuna cewa mamacin ya ci abincin rana da matarsa ta shirya masa a gida, bayan haka ya fara fama da matsanancin rashin lafiya. An garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa, sai dai likitoci suka tabbatar da mutuwarsa yayin da ake masa jinya.

Biyo bayan faruwar lamarin, jami’an bincike daga Sashen ’Yan Sanda na Jahun suka kama matar mamacin a matsayin babbar wadda ake zargi. A yayin tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa cewa ta saka maganin bera (rat poison) a cikin abincin mijinta. Ta kara da bayyana cewa ta tura ɗan uwanta domin sayo mata gubar da aka yi amfani da ita.

Wadda ake zargin ta ce iyayenta ne suka tilasta mata auren, abin da ta bayyana a matsayin dalilin da ya kai ta aikata wannan danyen aiki.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa ya bayar da umarni a mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Dutse domin zurfafa bincike. Bayan kammala binciken, za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.

Rundunar ’Yan Sanda ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da neman hanyoyin shari’a wajen warware matsalolin iyali da na aure.

Haka kuma, rundunar ta gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, tana mai jaddada cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da mummunan sakamako da ba za a iya gyarawa ba.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta tabbatar wa jama’a kudurinta na tabbatar da adalci da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.

Comments (0)
Add Comment