Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta yi wa Jam’iyyar NDC rajista.
Mai shari’a Isah Dashen ya ce, an yanke hukuncin farko ba tare da sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba, lamarin da ya sa hukuncin ya saɓa wa tanadin doka.
Kotun ta kuma amince da buƙatar Jam’iyyar PMP, wadda ta ce rajistar NDC ta shafi haƙƙinta saboda tambarin da aka yi amfani da shi.
Alƙalin ya umarci a mayar da komai yadda yake kafin hukuncin da aka yanke a watan Disamban 2025, sannan a sake fara sauraron shari’ar daga farko tare da haɗa INEC, NDC da PMP a matsayin ɓangarorin da abin ya shafa.
Hakan na nufin duk matakan da INEC ta ɗauka bisa tsohon hukuncin, ciki har da rajistar NDC, za su tsaya har sai an kammala shari’ar.