Kotu ta tsare mata kan zargin kashe jaririn mijinta mai kwanaki uku

Kotun Majistire mai lamba 2 da ke Kano ta bayar da umarnin tsare wata matar aure mai suna Zayya Magaji bisa zargin kashe jaririn mijinta mai kwanaki uku da haihuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin matar da haddasa mutuwar jaririn ne ta hanyar amfani da guba, duk da cewa ta musanta aikata wannan laifi a gaban kotu.

Wacce ake tuhuma, mazauniyar ƙauyen Danbamgo da ke ƙaramar hukumar Kabo a Jihar Kano, an gurfanar da ita ne ta hannun Lauyan Gwamnati, Barista Muhammad Aliyu.

A cewar mai gabatar da ƙara, an riga an miƙa fayil ɗin shari’ar zuwa Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano domin samun shawarar doka kafin ci gaba da shari’ar.

Mai shari’a Auwal Yusuf, wanda ya jagoranci zaman kotun, ya amince da buƙatar dage shari’ar tare da bayar da umarnin tsare wacce ake tuhuma a gidan yari har zuwa ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar.

Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Lamarin ya janyo hankalin al’umma, inda wasu ke bayyana damuwa kan yadda irin waɗannan al’amura ke ƙaruwa, tare da kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci da bin doka a irin waɗannan shari’o’i.

Comments (0)
Add Comment