Wata babbar kotu a Uyo ta yanke wa wani jami’in dan sanda mai mukamin kofur da kuma wani mai karbar kudin mota hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin hada baki da sace wani malamin makaranta domin neman kudin fansa.
Kotun ta samu Police Corporal Mbazigwe Chinedu Friday da Isaac Eddy Ndeesor da laifin hada baki, garkuwa da mutane da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, dangane da sace Elder Akara Johnson Mendie, mataimakin shugaban makarantar Community Secondary School Nkek da ke karamar hukumar Ukanafun. Lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Yuli, 2015, lokacin da wasu dauke da makamai suka tare motarsa yayin da yake dawowa daga coci tare da iyalansa, suka kuma tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Wanda aka sace ya shaida wa kotu cewa an rufe masa ido tare da kai shi wani daji, inda aka bukaci iyalansa su biya kudin fansa na naira miliyan 50 tare da yi masa barazanar kisa. Daga bisani an ce iyalansa sun biya naira dubu dari biyu kafin a sake shi a garin Bori na Jihar Rivers, inda ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda kafin a mayar da shi gidansa.
A cikin bayanan da ya bayar, kofur din ya amsa cewa ya taka rawa a satar, yana mai cewa wani da ya sani ne ya tuntube shi tare da zargin cewa wani “mai girma” ne ya bukaci a sace malamin. Ya kuma amince cewa ya yi amfani da motarsa wajen tare wanda aka sace, sannan daga baya ya dauke shi zuwa wani daji a Ogoni. Hukumomi sun ce an gano bindiga kirar gida, harsasai da sauran kayayyaki a gidansa.
Shi ma mai karbar kudin motar ya amsa cewa sun jira wanda aka sace kusa da gidansa bayan samun labarin zai dawo daga coci, inda ya kuma amince da satar wayar salularsa, wadda aka gano ta ne ta hanyar bibiyar na’ura, lamarin da ya kai ga cafke shi.
A hukuncinsa, Mai shari’a Nsemeke Daniel ya nuna rashin jin dadinsa kan tsawon lokacin da aka dauka ana sauraron shari’ar, wadda aka fara a 2016 aka kammala a 2026. Ya ce hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakk ba, tare da yin watsi da ikirarin cewa kazafi aka musu. Kotun ta yanke musu hukuncin daurin shekaru biyar kan hada baki, shekaru bakwai kan mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, sannan ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, tana mai cewa za a rataye su har sai sun mutu.