Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Ilorin, Jihar Kwara, ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen mutane biyar da aka samu da laifin fashin bankunan Offa na shekarar 2018, tare da tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke musu.
Alƙalan kotun uku sun amince baki ɗaya da hukuncin Babbar Kotun Jihar Kwara, wadda ta yanke wa waɗanda aka samu da laifi hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mutanen biyar, Niyi Ogundiran, Salawu Azeez, Ibikunle Ogunleye, Ayoade Akinnibosun da Adeola Abraham, an same su da laifin fashi da makami, kisan kai da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamnatin Jihar Kwara ta ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta ga wani kuskure a shari’ar ba, inda ta yanke hukuncin cewa gwamnati ta tabbatar da tuhumar da ake yi musu.
Kotun ta kori dukkan hujjojin ƙorafin da suka gabatar, tare da umarnin mayar da su gidan yari don ci gaba da zaman hukuncin da aka yanke musu.
Tun da farko, Babbar Kotun Jihar Kwara ta yanke hukuncin ne bayan shari’ar da ta ɗauki kusan shekaru shida, inda alkalin ya ce waɗanda aka yanke wa hukunci sun karya doka tare da dogaro da alaƙarsu da masu iko a wancan lokaci.
Fashin bankunan Offa na watan Afrilun 2018 ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 32, ciki har da ‘yan sanda tara, lamarin da ya sa aka ɗauke shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi muni a tarihin fashin banki a Najeriya.