Kotun Birtaniya Ta Wanke Diezani Alison-Madueke Daga Duk Zarge-Zargen Cin Hanci

Tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, ta samu nasara a shari’ar da ake yi mata a Birtaniya, bayan alkalai a Kotun Southwark Crown da ke Landan sun wanke ta daga dukkan tuhume-tuhume shida da suka haɗa da cin hanci da kuma haɗa baki wajen karɓar cin hanci.

Bayan shafe watanni ana sauraron shari’ar, alƙalan kotun sun yanke hukuncin cewa ba ta da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da masu gabatar da ƙara na Birtaniya suka kawo mata. Haka kuma, an wanke babban jami’in kamfanin mai, Olatimbo Ayinde, da kuma ɗan’uwanta, Doye Agama, daga zarge-zargen da ake yi musu.

Tun da farko, masu gabatar da ƙara sun zargi Diezani da karɓar wasu kuade daga wasu ‘yan kasuwar mai domin samun kwangilolin gwamnati a lokacin da take riƙe da muƙamin minista tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015, amma ta musanta dukkan zarge-zargen.

Comments (0)
Add Comment