Kotun ECOWAS ta dakatar da gwamnatin shugaba Buhari daga hukunta masu amfani da Twitter

Kotun ECOWAS dake Abuja ta dakatar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari daga hukunta masu amfani da Twitter.

Bayan gwamnatin tarayya ta haramta Twitter, yan Najeriya da dama suna tsallake haramcin ta hanyar amfani da VPN.

Amma ofishin babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, yayi barazanar hukunta wanda suke take dokar haramcin.

Kazalika, hukumar yada labarai ta kasa ta umarci dukkan gidajen rediyo da na talabijin su rufe shafukansu na Twitter.

Kungiyar SERAP tare da wasu yan Najeriya 176 sun kalubalanci matakin gwamnati a kotun ta ECOWAS. A hukuncin da ta yanke a yau, kotun ta hana gwamnati ta ci tara ko cin zarafi ko wulakanci ko kama ko gurfanar da masu amfani da Twitter.

Comments (0)
Add Comment