Kotun Legas ta yankewa shugaban makaranta ɗaurin rai-da-rai kan lalata da ɗaliba ’yar shekara 6

Wata kotun musamman da ke sauraron laifukan cin zarafi da rikicin cikin gida a jihar Legas ta yanke wa wani mai makaranta, Benson Arinze, hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samunsa da laifin lalata da wata ɗaliba mai shekara shida.

Rahotanni sun bayyana cewa Mai Shari’a Abiola Soladoye ce ta yanke hukuncin ranar 20 ga watan Mayun 2026 bayan kotun ta tabbatar da cewa an same shi da laifin cin zarafin yarinyar ta hanyar lalata da ita.

An bayyana cewa Arinze, wanda shi ne mamallakin makarantar Nurtured Brooks Nursery and Primary School da ke yankin Ibeju-Lekki a jihar Legas, ya aikata laifin ne a harabar makarantar.

A cewar masu gabatar da ƙara, mutumin ya yi amfani da lokacin da yarinyar ta rage a makaranta bayan an tashi domin aikata laifin.

Lamarin ya fito fili ne bayan mahaifiyar yarinyar ta lura da wasu sauye-sauyen hali tare da tambayarta abin da ke faruwa.

Daga nan ne yarinyar ta bayyana yadda ake yawan cin zarafinta a cikin makarantar, lamarin da ya sa mahaifinta ya kai ƙara ofishin ’yan sanda na Elemoro Division.

A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Soladoye ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, yayin da shaidun da ɓangaren wanda ake tuhuma suka gabatar suka kasa wanke shi.

Kotun ta kuma bayar da umarnin sanya sunan mutumin cikin kundin masu aikata laifukan cin zarafin mata da yara na jihar Legas kamar yadda dokar hukumar yaƙi da cin zarafi ta shekarar 2021 ta tanada.

Hukumar Yaƙi da Cin Zarafi da Rikicin Cikin Gida ta jihar Legas ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da kai rahoton duk wani nau’in cin zarafi, tana mai cewa lokaci ya yi da za a karya al’adar yin shiru kan irin waɗannan laifuka.

Comments (0)
Add Comment