Wani bangare na kungiyar Afenifere mai biyayya ga marigayi Chief Ayo Adebanjo ya soki matakin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dauka na hana waka “Tell Your Papa” ta Eedris Abdulkareem, tana mai cewa hakan cin zarafin ‘yancin fadar albarkacin baki ne a tsarin dimokradiyya.
A wata sanarwa da Oba Oladipo Olaitan da Justice Faloye suka sanya wa hannu, kungiyar ta ce wakar ba ta da cin fuska, sai dai martani ne bisa furucin da dan shugaban kasa, Seyi Tinubu, ya yi kan halin da kasar ke ciki.
Afenifere ta ce matakin hana wakar ya nuna alamun jagoranci da ke kaucewa gaskiya da natsuwa, yana kuma nuna an yi watsi da muradun jama’a da ’yancin kirkira da fadar ra’ayi.
Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan tsaro a kasa, tana mai cewa sama da mutane 1,420 sun mutu sakamakon rikice-rikice a watanni ukun farko na shekarar 2025, tare da sace mutane 537, yayin da ta bukaci kafa ’yan sanda na jihohi da kuma sake fasalin tsarin mulki don tabbatar da adalci da zaman lafiya a Najeriya.