Kungiyar Mai Da Zaman Lafiya Ta Matan Borno Ta Yabawa Sojojin Kasarnan Kan Kubutar Da Wasu ‘Yan Matan Chibok

Kungiyar mai da zaman lafiya ta matan Borno ta yabawa sojojin kasarnan kan farmakin da ‘yan ta’adda suka kai a dajin Sambisa tare da kubutar da wasu daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa a yau ta hannun sakatariyar ta, Amina Mele, ta ce jihar za ta fara samun cikakken zaman lafiya nan ba da dadewa ba.
Amina Mele ta ce kungiyar ta yi matukar farin ciki da ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a jihar, musamman aikin kakkabe mayaka a dajin Sambisa.
Ta yabawa sojojin da suka bankado wajen ajiyar kayan aikin ISWAP na karkashin kasa wanda ya kai ga kwato manyan makamai da alburusai.
Idan dai za a iya tunawa, kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Ibrahim Ali, a ranar 6 ga watan Mayu, ya sanar da kubutar da wata dalibar Chibok mai suna Saratu Dauda.
Ya ce ya zuwa yanzu an kubutar da ‘yan matan Chibok 183 da aka yi garkuwa da su, yayin da sauran 93 suka rage.

Comments (0)
Add Comment