Wata sanarwa da Kungiyar Masu Cajin Waya da Wayar Hannu ta Karamar Hukumar Auyo a Jihar Jigawa ta fitar, ta nuna karin kudin wasu daga cikin ayyukan da mambobinta ke yi ga al’umma.
A cikin sanarwar da aka manna a wani wuri na kasuwanci, kungiyar ta bayyana cewa sabon tsarin farashin zai fara aiki daga ranar 5 ga watan Yuni, 2026, sakamakon yadda farashin kayayyaki da sauran abubuwan gudanar da sana’a suka tashi.
Sabbin kudaden da aka kayyade sun hada da cajin kwamfuta kan Naira 300, cajin power bank Naira 250, yayin da cajin wayoyin Android zai kasance Naira 200. Haka kuma, cajin kayan aiki kamar keypad, MP3, fitila da baturi an sanya shi a Naira 150.
Kungiyar ta bukaci abokan hulda da masu anfani da ayyukanta da su yi hakuri tare da fahimtar dalilan da suka sa aka dauki wannan mataki, tana mai cewa karin kudin zai taimaka wajen ci gaba da gudanar da sana’ar yadda ya kamata.
Matakin ya jawo martani daga wasu mazauna yankin, inda wasu ke ganin karin kudin ya yi daidai da halin tsadar rayuwa da ake fama da shi a halin yanzu, yayin da wasu ke nuna damuwa kan yadda karin zai kara wa jama’a nauyi.