Kungiyar ‘yan kwadago ta NLC ta soki taɓarɓarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

Kungiyar ‘yan kwadago ta Nigeria Labour Congress (NLC) ta bayyana damuwa kan taɓarɓarewar tattalin arziki da matsalar tsaro a Najeriya, tana mai cewa miliyoyin ‘yan ƙasa na fama da matsin rayuwa sakamakon manufofin gwamnati da suka ƙara jefa jama’a cikin talauci da wahala.

A cikin saƙon Sallah da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu, NLC ta ce ya kamata shugabanni su mayar da hankali wajen kare rayuka da samar wa jama’a abinci, aikin yi, lafiya da ilimi maimakon manufofin da ke fifita riba kan walwalar talakawa.

Ƙungiyar ta kuma danganta matsalar tsaro da gazawar shugabanci, tana mai cewa hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da rikice-rikicen cikin gida sun ƙara jefa al’umma cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

NLC ta kuma yi gargaɗin cewa ‘yan Najeriya za su yi amfani da zaɓen 2027 wajen hukunta shugabannin da suka gaza cika alƙawuran da suka ɗauka.

Comments (0)
Add Comment