Kungiyoyin Mai Sun Shirya Shiga Yajin Aiki Kan Rikicin Dangote da NUPENG

Ƙungiyar masu rarraba mai da haɗin gas na Najeriya (NOGASA), masu gidajen sayar da mai (PETROAN), da kuma kungiyar direbobi ta (NARTO) sun bayyana aniyarsu ta shiga cikin yajin aikin da NUPENG ta sanar.

Wannan na zuwa ne bayan matakin direbobin manyan motoci na NUPENG da suka nuna adawa ga shirin kamfanin Dangote na fitar da manyan motoci dubu huɗu masu amfani da iskar gas kai tsaye don rabon mai.

Shugaban NOGASA, Bennett Korie, ya umarci masu rarrabawa da su dakatar da kai mai ga wuraren amfani idan tattaunawar gwamnati ta gaza cimma matsaya kafin safiyar gobe.

Kungiyoyin sun ce yayin da suke ganin gagarumar gudunmawar da matatar Dangote za ta bayar, suna da damuwa kan yadda hakan zai haifar da asarar ayyukan yi da durkusar da daruruwan masu cin gajiyar harkar rarraba man fetur.

Comments (0)
Add Comment