Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i na Najeriya, wato Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) da Non-Academic Staff Union of Educational and Associated Institutions (NASU), sun bayyana cewa za su gudanar da zanga-zangar kasa baki ɗaya a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, saboda rashin biyan alawus da wasu hakkokin ma’aikata da Gwamnatin Tarayya ta kasa biyan su tsawon lokaci.
A wata sanarwa da shugabannin ƙungiyoyin suka fitar bayan taron majalisar zartarwarsu ta ƙasa (NEC), sun ce za a gudanar da zanga-zangar ne a dukkan jami’o’in tarayya da na jihohi domin nuna bacin rai da gajiya da yadda gwamnati ke yi watsi da bukatun su.
Kungiyoyin sun zargi gwamnati da kasa cika yarjejeniyoyin da suka yi a baya, ciki har da:
- Biyan bashin alawus na aiki da aka ci ba a biya ba (earned allowances);
- Sabunta albashi bisa karin mafi ƙarancin albashi (minimum wage adjustment);
- Sakin albashin da aka hana ma’aikata lokacin yajin aiki a baya.
SSANU da NASU sun ce wannan rana ɗaya ta zanga-zanga gargadi ce, kuma idan gwamnati ta ci gaba da yin shiru, za su komar da yajin aiki na gaba ɗaya don tilasta gwamnati sauraren su.
Kungiyoyin sun kuma zargi gwamnati da nuna wariya a tsakanin ma’aikatan jami’a, inda ake fifita malaman jami’a (academic staff) fiye da sauran ma’aikata (non-academic staff). Sun ce wannan rashin adalci yana rage kwarin gwiwar ma’aikata tare da haifar sharin kan gado a tsarin ilimi na jami’o’i.
Daga ƙarshe, SSANU da NASU sun roƙi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar mataki kan wannan batu domin guje wa barkewar sabon yajin aiki da ka iya dakatar da harkokin jami’o’i a fadin ƙasa.