Kwamandojin Boko Haram biyu sun mika wuya ga sojojin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF

Wasu kwamandojin Boko Haram biyu, Ibrahim Muhammed da Auwal Muhammed, sun mika wuya ga sojojin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF da ke Monguno a Jihar Borno.

Rundunar MNJTF ta hada da kasashe da dama da suka hada da rundunar sojin kasashe irin su Benin, Kamaru, Chadi, Nijar da muma Nijeriya.

Rundunar tana da hedikwata a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi kuma tana yaki da ta’addancin Boko Haram.

Shugaban yada labaran rundunar, Lafkanar Kanal Abubakar Abdullahi ne, ya bayyana a jiya Talata, inda ya bayyana cewa Kwamandojin biyu sun mika wuya ne bayan sun shafe fiye da shekara 10 suna aikata ta’addanci. Abdullahi ya kuma bayyana cewa, a yayin bincike, maharan biyu sun amince za su taimaka wa rundunar da bayanai don samun nasarar dakile abokan aikinsu.

Comments (0)
Add Comment