Abuja, 22 ga Janairu, 2026 – Mambobin kwamitin gudanarwa na Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) sun rubuta takarda ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, suna neman a cire Farfesa Abdullahi Saleh Usman daga shugabancin hukumar.
A cikin takardar, mambobin sun zargi shugaban da cin hanci, rashin iya aiki, kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, da bayar da kwangiloli fiye da iyakar kasafin da aka amince da shi. Sun ce ci gaba da kasancewarsa a ofis zai jefa shirye-shiryen Hajji da gudanarwar hukumar cikin haɗari, har ma zai iya kawo matsala ga diflomasiyyar Najeriya.
Mambobin da suka sanya hannu a takardar sun haɗa da Farfesa Abubakar Yagawal, Yarima Anofi Elegushi, Yarima Aliu Abdulrazaq, Farfesa Muhammad Umaru Ndagi, Alhaji Abba Jato Kala, Sheikh Muhammad Bin Uthman, Dr Tajudeen Abefe Oladejo, Hajiya Aishat Obi Ahmed, Hajiya Zainab Musa, Farfesa Musa Inuwa Fodio da Farfesa Mahfouz Adedimeji.
Shugaban hukumar ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa mafi yawan korafe-korafen na fitowa ne daga masu ƙiyayya da rashin jin daɗi daga wasu mambobi.