Kwamitin Sasanto na Jam’iyyar APC ya gudanar da ganawa da Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam (Dr.) Umar A. Namadi, FCA, a wani zama da ya nuna ci gaba da haɗin kai, tuntuba da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnatin jihar da jam’iyyar APC.
A yayin ganawar, an tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban jam’iyyar da kuma yadda za a ci gaba da tabbatar da haɗin kai tsakanin shugabannin gwamnati da na jam’iyya domin ci gaban jihar.
Mambobin kwamitin sun yabawa Gwamna Umar Namadi kan salon jagorancinsa da kuma kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen aiwatar da ayyukan raya kasa da inganta walwalar al’ummar Jigawa.
A nasa bangaren, Gwamnan ya jaddada muhimmancin haɗin kai da tuntuba a tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da jam’iyyar APC domin ciyar da jihar gaba.
Ganawar ta kara nuna aniyar bangarorin biyu na ci gaba da inganta hadin kai da tabbatar da nasarorin jam’iyyar APC a Jihar Jigawa.
Ko kuna ganin wannan kwamati zai lallashi wadanda suka yi fushi?